Home » Majalisar Wakilai Ta Musanta Karɓar Kuɗi Kan Saka Dokar Ta-ɓaci A Ribas

Majalisar Wakilai Ta Musanta Karɓar Kuɗi Kan Saka Dokar Ta-ɓaci A Ribas

Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun.

Wasu ƙungiyoyi na zargin majalisar da yin ƙasa a gwiwa wajen yanke hukunci kan lamarin.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa yawancin mambobin majalisar sun goyi bayan matakin ne domin kare dimokuraɗiyya da kuma tsare muradun al’ummar Jihar Ribas.

“Mun yanke shawarar ne bisa kishin ƙasa, haɗin kan siyasa, zaman lafiya, da kare dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Ya ce ya yi mamakin yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke baza jita-jita cewa an tilasta musu su amince da dokar ta-ɓaci tare da karɓar daloli.

A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa ’yan majalisa suna aiki ne don ganin an samar da tawagar sulhu kafin wa’adin dokar ta-ɓacin ta ƙare.

Ya jaddada cewa dole ne a kare dimokuraɗiyya a Najeriya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?