Kotun shari’ar Muslunci da ke zaman ta a Sharaɗa Hisbah a Kano, ƙarkashin mai Shari’a Tamim Sani Tamim Hausawa, ta sake aike wa da ƴar TikTok ɗin nan Ruƙayya Ibrahim wacce akafi sani da Ummin Mama, gidan gyaran hali da tarbiya ,bisa zargin ta da laifin yaɗa bidiyon Baɗala da tsaraici a kafar TikTok .
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce ta kama Ummin Mama, a cikin gidan namun daji dake Zoo road, daga bisani ta miƙa ta ga ƴan sanda su kuma suka cike mata takardun tuhuma tare da gurfanar da ita a gaban kotun da zarge-zargen da ake yi mata.
Bayan karanta wa Ummin Mama, ƙunshin tuhumar da ake yi mata na yaɗa bidiyon baɗala gami da wallafa tsaraici a shafukan sada zumunta, ta amsa laifukan , inda Kotun ta sake aikewa da ita gidan gyaran hali zuwa ranar Litinin 24 ga watan Maris ɗin 2025, domin yanke hukunci.
Bayan fitowa daga kotun ne Matashiya Ruƙayya Ibrahim mai laƙabin ummin Mama Ba mai yi sai Allah, ta ce da zarar ta fito daga gidan yarin wa’azi za ta koma a shafukan sada zumunta sanye da Hijabi, duba da wahalar da ta sha a gidan yarin.
Idan ba a manta ba Muhasa TV Radio 92.3, ta ruwaito muku cewa, Wani mutum ya Yi wa alkalin dake Sauraren shari’ar ta yin bashi Dalolin Amurika don ya saki yar TikTok din, amma alkalin kotun Sani Tamim Hausawa yayi fatali da tayin cin hancin .