Majalissar dinkin duniya ta ce miliyoyin mutane a Najeriya na iya fuskantar matsananciyar yunwa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa miliyoyin ’yan Najeriya na iya fuskantar matsananciyar yunwa a watanni masu zuwa sakamakon matsalar tsaro, rikice-rikice da kuma tsadar rayuwa da ke ƙaruwa a faɗin ƙasar.

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA), ta ce iyalai da dama za su shiga wani yanayi da ka iya zama mafi muni a shekarun baya-bayan nan.

Lokacin ƙarancin abinci, wanda yawanci ke tsakanani a watan Yuni zuwa Agusta kafin girbi, lokaci ne da abinci ke ƙaranci kuma farashi ke tashin gwauron zabi.

A cewar OCHA, kusan mutane miliyan 35 a Najeriya, wato kusan kowane mutum ɗaya cikin mutane bakwai na iya fuskantar matsanancin ƙarancin abinci a wannan lokaci.

Hukumar ta ce Arewacin Najeriya ne zai fi fuskantar wannan matsala sakamakon hare-haren ’yan bindiga, rikice-rikice da kuma yawaitar mutanen da suka rasa matsugunansu.

OCHA ta yi gargaɗin cewa idan ba a kai ɗauki cikin gaggawa ba, iyalai da dama za su rage yawan abincin da suke ci, su sayar da kadarorinsu ko kuma su cire ’ya’yansu daga makaranta domin samun abin rayuwa.

Majalisar ta kuma nuna damuwa kan ƙaruwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ƙananan yara.

Ta bayyana cewa kimanin yara miliyan 6.4 a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na iya fama da matsananciyar tamowa a bana.

Ƙungiyoyin agaji na jin-ƙai sun yi kira ga ƙasashen duniya da su gaggauta bayar da tallafi domin taimaka wa al’ummomin da matsalar ka iya shafa.

OCHA ta ce shirin agajin jin-ƙai na Najeriya bai samu ko rabin kuɗaɗen da ake buƙata ba.

Hukumar ta ƙara da cewa duk da an fara bayar da wasu tallafin gaggawa ta hannun Asusun Agajin Jin-ƙai na Najeriya, har yanzu ana buƙatar ƙarin kuɗi da tallafi domin hana matsalar ƙara muni.

Post masu alaƙa

Ebola: An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Congo

Tinubu ya yaba wa gwamnonin APC kan zaɓen fitar da gwani

Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC