Ƴan sandan Kano sun ƙwato motocin sata 3 tare da kama mutane uku da ake zargi

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama mutane uku da ake zargi da satar motocin jama’a, tare da ƙwato motoci uku da ake zargin na sata ne.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Abel Nanlir Nafa daga Abuja, Stephen Wanneh daga jihar Kaduna, da Habiba Mohammad daga Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, sun kama waɗanda ake zargin kan wata mota ƙirar Toyota Camry, da aka sato daga jihar Enugu, sannan suka sake ƙwato wasu motocin biyu a jihar Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano , CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka da kuma ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai