Majalissar Zartarwa ta amince da gina sabuwar fadar Sarkin Dutse kan Biliyan 2.77

Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar A. Namadi, FCA, ta amince da jerin manyan tsare-tsare, kwangiloli da shirye-shiryen ci gaba da za su inganta sufuri, noma, ilimi, samar da ruwa, da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Ɗaya daga cikin manyan matakan da majalisar ta ɗauka shi ne amincewa da sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) tsakanin Gwamnatin Jihar Jigawa da kamfanin Rano Air domin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci tsakanin Dutse da Abuja, wanda ake sa ran zai fara nan take.
Har ila yau, Majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina sabuwar Fadar Sarkin Dutse kan kuɗin Naira biliyan 2.77, domin samar da fada ta zamani da ta dace da martabar.
A fannin addini kuwa, Majalisar ta amince da karɓar bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa karo na 41, wadda za a gudanar a Dutse daga ranar 14 zuwa 30 ga Nuwamba, 2026

Post masu alaƙa

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

An Kashe Makiyaya 50 An Sace Shanu Sama da Dubu 2 A Kaduna — MACBAN

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur