Yusuf Buhari ya lashe zaɓen takarar majalisar tarayya a APC

Yusuf Buhari, ɗan tsohon shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari, ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaɓe na mazabar, Lawan Garba, ya ce Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 17,342, inda ya doke abokin takararsa, Auwalu Musa Daura, wanda ya samu ƙuri’u 480, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Saboda haka Garba ya ayyana Yusuf Buhari a matsayin ɗan takarar jmajalisar tarayya a am’iyyar APC na mazaɓar Daura/Sandamu/Mai’adua a zaɓe mai zuwa.

Sai dai a wata hira da manema labarai, abokin takarar Yusuf Buharin, Auwalu Lawan Daura, wanda ɗan tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Daura ne, ya yi watsi da sakamakon zaɓen, inda ya yi zargin an tafka maguɗi.

A jawabin da Yusuf ya yi bayan nasarar, ya buƙaci magoya bayansa da abokin takarar su haɗa kai wajen samar da ci gaba a yankin.

Post masu alaƙa

Muhammad Babandede ya gabatar da muhimman shawarwari kan karfafa tsaron yankin arewa maso yamma

An gabatar da jirage marasa matuƙa na ARCO Worldwide Services Limited domin ƙarfafa aiyukan tsaro a Arewa maso Yammancin Nijeriya.

An karrama Muhammad Babandede, OFR, OCM, da wasu kungiyoyi kan aiyukan jin kai ga marasa galihu.