Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa.
Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin.
Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki.
“A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”
“Bayan na tura mata kudi, kiranmu na ƙarshe shi ne lokacin da ta bar wajen sayar da maganin kusan ƙarfe 6 na yamma. Daga nan ban sake samun ta ba.”
“Na ci gaba da kiranta har zuwa safiyar ranar Lahadi, sai na ɗauka cajin wayarta ne ya ƙare.”
- Gwamnan Kaduna Uba Sani Ya Yi Wa Ma’aikatan Manyan Makarantu Karin Kashi 70 A albashi
- Gwamnan Kano Ya Buƙaci NBC Ta Sa Ido Kan Kafofin Yaɗa Labarai Na Intanet
Idris, wanda ya farfado daga suma a ranar Talata bayan girgizar da lamarin ya haifar, ya ce daga baya ya gano cewa marigayiyar ta hau babur din haya kusan ƙarfe 6:30 na yamma a ranar Asabar, amma daga bisani wasu suka kai mata hari don su kwace wayarta.
“Alamu sun nuna matse hannayenta aka yi, alamar cewa an tilasta mata yayin da ake ƙoƙarin kwace wayar.”
Idris ya ce bayan ta suma, sai barayin suka sace wayarta suka jefar da ita a gefen titi kusa da filin Idi na Mallawa a Tudun Wada Zariya.
Ya ce wani mai tausayi da ya same ta ya garzaya da ita zuwa wani asibiti, daga bisani aka tura ta zuwa Asibitin Koyarwa na ABU, Shika, inda aka tabbatar da rasuwarta.
Mijinta ya ce Hadiza ta rasu watanni uku bayan rasuwar ’yar uwarta, wadda ta ɗauki ‘ya’yanta uku a matsayin nata.