Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ake sa ran zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar a kwanakin baya.
Babban lauyan gwamnatin tarayyar Mista Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan a jihar Ekiti a jiya Talata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Mista Fagbemi ya ce ba gudu ba ja da baya a kan shirin aiwatar da hukuncin kotun ƙolin kan cin gashin ƙananan hukumomin Najeriya.
Mista Fagbemi ya jaddada cewa gwamnati za ta yi nazarin dokokin jihohi a kan zaɓen ƙananan hukumomi tare da duba dalilin da ya sa wasu jihohin ke neman kin gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara.
Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu sama da ƙananan hukumomi 164 ne a jihohi takwas ba su yi zaben ba.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, akwai yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da hukuncin kotun ƙolin a kan cin gashin kai na ƙananan hukumomi nan da ƙarshen watan nan na Oktoba.
- Za A Yi Zaben Kananan Hukumomi Ranar Asabar-Majalisar Kano
- Babban Layin Wutar Lantarkin Da Ke Kawo Wuta Arewa Ya Sake Ɗaukewa
wannan na nufin gwamnatin tarayyar za ta iya riƙe kason kuɗin ƙananan hukumomin da ba a yi zaɓe ba, kamar yadda hukuncin kotun ya ayyana.
Kawo yanzu dai ba a yi zaɓen kananan hukumomi ba a jihar Katsina da Zamfara da Nasarawa da Ondo, da Osun da Ogun da Cross Rivers da Kano.
Hukuncin kotun da aka yi a watannin da suka gabata ya nuna cewa, saɓa doka ne gwamnonin jihohi su ci gaba da karɓa ko riƙe kason kuɗaɗen ƙananan hukumomi a ƙarƙashin asusun haɗin gwiwa.