An Dakatar Da Tallan Maganin Gargajiya A Fina-finai A Kano 

Hukumar Tace Fina-finai Da Dab’i Ta Jihar Kano ta bayyana dakatar da nuna duk wani tallan maganin gargajiya a fim tare da masu yawo a tituna da lasifika a ciki a jihar. 

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne A wani yunkuri na tabbatar da bin ka’idoji tare da inganta sana’ar masu sayar da maganin gargajiya a Kano dakuma masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Shugaban Hukumar, Alh Abba El-mustapha ne ya bayyana cewa yawancin tallace-tallacen da ake yi a tituna da lasifika ko kuma a cikin Fina-finan na karya dokokin Hukumar, wadanda ke bukatar a tace su kafin a fitar da su ga jama’ae gari.

Alh. Abba El-Mustapha ya bayyana hakan ne a ofishinsa yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai.

Hukumar ta umurci duk masu tallan Maganin gargajiya a tituna da lasifika tare da cikin fina-finai da su miko tsarin tallace tallacen magungunansu domin a tantance tare da samun sahalewar Hukumar a cikin mako daya, tun daga Laraba 21 Ga Mayu, 2025.

Jawabin ma shugaban hukumar ya bayyana cewa rashin bin wannan doka na iya janyo fushin hukum.

El-Mustapha ya kuma yi kira ga dukkanin tashoshin talabijin tare da Hukumar Kula da kafafen yada Labarai ta Kasa (NBC) da su goyi bayan kokarin da hukumar ke yi wurin tabbatar da a na bin dokar Hukumar domin inganta tarbiyya a tsakanin al’ummar Kano.

Kamar yadda Malam Abdullahi Sani Suleiman jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ya turawa manema labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *