An kwantar da firaministan Isra’ila a asibiti saboda rashin wadataccen ruwa a jikinsa

Firaministan Isra`ila Benjamin Netanyahu ya shafe daren da ya gabata a asibiti, a dalilin abin da aka ce rashin isasshen ruwa a jiki.

Ofishinsa ya ce an dage taron da ya saba yi na mako-mako a ranar Lahadin nan har sai washegari, Litinin, duk da cewa Netanyahun ya bayyana cewa ya wartsake.

Wannan shi ne karo na biyu da ake kwantar da shi a asibiti ya shafe dare, a cikin wata tara.

A watan Oktoba an kwantar da shi a asibiti inda ya shafe dare, sakamakon jigata da ya yi bayan ya yi azumi.

Post masu alaƙa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.