Matasa a Jihar Neja sun kaddamar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Masu zanga-zangar sun fantsama kan manyan titunan jihar, ciki har da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Matasan da ke tafe suna rera wakar adawa da tsare-tsaren gwamnati sun daga kwalaye masu dauke da rubutu a jikinsu da ke nuna bacin ransu kan halin tsadar rayuwa a Najeriya.
- Turji Ya Jaddada Cewa Matawalle Na Tallafwa Ta’adanci
- Gwamnatin Kano Ta Mika ‘Yan Cirani 49 Ga Iyalansu
A jikin kwalayen sun yi rubuce-rubuce da dama, da suka hada da, ‘A soke tsare-tsere masu kuntata wa jama’a; ‘tura ta kai bango’; ’ ‘Mu Ba Bayi Ba Ne A kasarmu’; ‘Ba Za Mu Jere Wannan Wahalhalun Ba’, ‘Dole A Dawo da tallafin man fetur’.
Gwamnatin tarayya da na jihohi sun yi yunkuri iri-iri da zummar dakatar da zanga-zangar, suna masu cewa zauna-gari-banza da makiya dimokuradiyya za su iya kwace ta, wadda ka iya janyo asara ga kasar.
A baya dai rahotanni sun tabbatar da cewa za a fara zanga-zangar ne ranar Alhamis, 1 ga watan Agustan, 2024.