Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar matashin da ake zargi da halaka wani jami’in soja ta hanyar daba masa wuka bayan ya kwace wayarsa.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ne ya tabbatarwa da abokin aikin mu Mujahid Wada, a zantawar da suka yi ta wayar tarho da safiyar yau Litinin.
Ya lamarin ya faru ne, lokacin da wani jami’in soja mai suna , Laftanar Commodore M. Buba, yake gyaran motarsa a ranar Lahadi, inda matashin ya yi yunkurin kwace wayarsa amma yaki bashi ,har ya soka masa wuka a kirjinsa wanda hakan yayi sanadiyar rasuwarsa.
Sai dai ya kara da cewa wani jami’in soja ya kawo masa daukin gaggawa amma wanda ake zargin ya caka masa wuka a hannu, inda mutane suka taso suka dinga dukansa wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.
An garzaya da jami’in sojan zuwa Asibitin Manaal, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa, daga bisani aka ɗauki gawarsa zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin 44 Nigerian Army Reference Hospital da ke Kaduna.
- Za Mu Bai Wa Manoma Cikakken Tsaro: Bello Matawalle
- Kungiyar SURE4U Ta Bayar Da Gudunmawar Kayan Aikin Lafiya A Babban Asibitin Hadejia.
DSP Mansur Ya ce yanzu haka kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, CP Rabi’u Muhammed , ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da gano sauran gungun wadanda suke aikata laifin.
Tuni ya tabbatar da cewa sun kama mutane da yawa dauke da makamai , kuma ana ci gaba da yin bincike a yankin da lamarin ya faru don jihar ta zauna lafiya.
Sai dai ya ce wadanda aka kama basu da alaka da matashin da ya rasa ransa, amma bincike ne kawai zai tabbatarwa.