Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur karo na biyar a watan Maris

A karo na biyar cikin watan Maris, Matatar Dangote ta sake ƙara farashin man fetur zuwa N1,275 kan kowace lita, daga N1,175 da ake sayarwa a farkon watan.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sabon farashin ya fara aiki daga tsakar daren ranar 21 ga Maris, kamar yadda sanarwar da matatar ta aika wa ’yan kasuwa da abokan hulɗarta ta nuna.

Rahotanni sun ce ƙarin farashin ya samo asali ne daga sauye-sauyen kasuwar mai ta duniya, musamman sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da ya shafi samar da makamashi.

Haka kuma, matatar ta ƙara farashin jigilar mai ta ruwa daga N1,512,648 zuwa N1,646,748 kan kowace tan, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 8.9 cikin ɗari.

Bincike ya nuna cewa farashin fetur daga matatar ya tashi daga N774 a farkon watan zuwa N1,275 a yanzu, wanda ke nuna karin sama da kashi 60 cikin ɗari cikin ƙasa da makonni uku.

Masana sun ce wannan hauhawar farashi na iya haifar da karin kuɗin sufuri da tsadar kayayyaki a faɗin ƙasar, yayin da kasuwar mai a Najeriya ke ci gaba da fuskantar sauye-sauye bayan cire tallafi.

Duk da haka, matatar ta ce matakin ya zama dole domin daidaita farashi da halin da kasuwar duniya ke ciki, tana mai jaddada cewa abubuwan da ke haddasa hakan sun fi ƙarfin ikon ta.

Post masu alaƙa

Matatar Man Dangote Ta Rage Farashin Fetur Zuwa N699

APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano

An Kama 420kg Na Fatar Dabbar Pangolin A Kano- Hukumar Kwastam.