Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba rancen naira miliyan dubu huɗu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba rancen naira miliyan dubu huɗu a matsayin rancen sayen ababen hawa ga ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi cikin shekaru uku da suka gabata.
Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin jawabi a bikin ranar ma’aikata ta bana, kamar yadda Gidan Rediyon Jihar Jigawa ya rawaito.
Ya ce kimanin ma’aikata dubu goma sha uku ne suka ci gajiyar rancen da nufin inganta rayuwarsu.
A ƙarshe, ya bayyana cewa kula da jin daɗin ma’aikata na aya daga cikin manufofin gwamnatinsa domin sauƙaƙa musu gudanar da aiki yadda ya kamata.

Post masu alaƙa

Sai ’yan Najeriya sun sayi litar man fetur N5,000 idan Tinubu ya zarce

Gwamnan Kano ya naɗa Barista Hafsat Kutama shugabar hukumar PCACC

Rundunar yan sandan Kano ta kama mutane 10 da ake zargi da satar motoci tsakanin jihohi.