Ƴan bindiga sun sace sakataren ƙaramar hukumar Kibiya.

Wasu ƴanbindiga sun kai hari gidan sakataren ƙaramar hukumar Kibiya da ke jihar Kano tare da sace shi.

Shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Hon. Sabo Yusuf Usman ya shaida wa BBC cewa lamari ya faru ne ranar Juma’a da daddare a gidan sakataren da ke garin Dinya.

”Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da sakataren ke barci a gidansa”, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa lokacin da maharan suka zo sun tashi ɗan gidan sakataren da ke kwana a zauren waje, inda suka tilasta masa ƙwankwaso kofar gidan, sannan ya faɗa wa mahaifinsa cewa cikinsa na ciwo.

”Hakan kuwa aka yi, bayan ya ƙwanƙwasa mahaifin nasa ya ce wane ne? Sai ya ce shi ne (ɗansa), ya ce me ya faru? Sai ya ce cikinsa ne ke ciwo, nan take mahaifin ya buɗe ƙofa, daga nan maharan suka kama shi tare da ɗan nasa”, a cewar Hon Sabo.

Ya ƙara da cewa tuni dai jamai’an tsaro suka kai taimakon gaggawa, amma kafin zuwansu maharan sun tafi da sakataren bayan sun sako ɗan nasa.

A baya dai ba a san ƙaramar hukumar Kibiya da matsalar tsaro ba, amma an sha samun matsalolin hare-haren ƴanbindiga a ƙanana hukumomin Tsanyawa da Shanono da suka yi iyaka da jihar Katsina.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda