Matsalar Rashin Tsaro Na Neman Kassara Arewacin Najeriya– Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa

Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa ta ACF, ta nuna damuwarta kan yadda matsalar rashin tsaro ke neman kassara yankin Arewacin Najeriya, Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar Alhaji Bashir Muhhamd  Ɗalhatu Wazirin Dutse ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da ƙungiyar takai jihar Borno.

Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ƙara da cewa yanayin yadda ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin na Arewa abun tsoro ne.

ACF ta nemi mahukunta da su ɗauki matakan gaggawa da zasu kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ya addabi yankin.

Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ita ce babbar barazana da take addabar yankin. Musamman Jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina.

A baya baya ne dai Ƙungiyar ta dattawan Arewa ta gudanar da wani taro a Kaduna inda aka haɗa kan manyan Arewacin Najeriya domin nemo bakin zare da mafita ga yankin.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin daji

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023