Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen ƙasa a watan Janairun 2027, ana sa ran miliyoyin ‘yan ƙasa za su kaɗa ƙuri’a domin zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma ‘yan majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.
Lokacin da ‘yan Najeriya suka je rumfunan zaɓe a shekarar 2023, mutane da dama sun yi imanin cewa sabuwar fasahar gudanar da zaɓe da aka ƙaddamar, yawan matasa da suka fito kaɗa ƙuri’a, da kuma gasa ta musamman tsakanin manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa guda uku za su taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar.
Sai dai matsalolin fasaha da suka shafi shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na duba ko sakamakon zaɓe sun yi tasiri wajen rage amincewar jama’a da tsarin.
Daga bisani an ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe ɗaya daga cikin zaɓukan da suka fi zafi a tarihin Najeriya.
Manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), sun ƙalubalanci sakamakon a kotu. Sai dai a ƙarshe Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Shekaru huɗu bayan haka, Najeriya na sake komawa rumfunan zaɓe cikin wani yanayi da ya bambanta da na baya, ta fuskar siyasa da tattalin arziki.
An samu sauye-sauye a dokokin zaɓe, jam’iyya mai mulki ta faɗaɗa tasirinta a fagen siyasa, yayin da masu kaɗa ƙuri’a ke fuskantar sabbin ƙalubale da suka haɗa da tsadar rayuwa, matsalolin tsaro da kuma wutar lantarki.
Haka kuma, sabon rukuni na matasa masu jefa ƙuri’a na shirin taka muhimmiyar rawa a zaɓen.