A baya-bayan wasu jaruman Kannywood na ci gaba da ficewa daga wata ƙungiyar da wasu ƴan masana’antar suka kafa da nufin tallata Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC gabanin zaɓen 2027.
Mutum na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope, shi ne fitaccen jarumi Rabiu Rikadawa, wanda ya ce ya fita daga ƙungiyar saboda abin da ya kira ”rashin tabbas da rashin aiki da dokokin ƙungiya”.
Kafin Rikadawa an ga wasu fitattun jarumai da suka sanar da ficewarsu daga ƙungiyar, irin su Mansura Isa da fitaccen marubucin nan Ibrahim Birniwa da Yusuf Sasen fitaccen jarumi a masana’antar.

