Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci jagororin addinin Musulunci da su yi amfani da su yi amfani da ranar Sallah domin yi wa ƙasar addu’a samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
Tinubu ya bayyana haka a saƙonsa na Sallah, wanda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, inda a ciki ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen ƙaunar ƙasar da son juna.
Ya kuma buƙaci Musulman Najeriya da su ci gaba da koyi da abubuwan da suka koyi a watan mai tsarki, wanda ya ƙarfafa “imani da tausayi da haɗin kai a tsakanin al’umma.”
“Akwai darussa da yawa da za mu koya daga watan Ramadan, musamman a wannan lokacin da muke ciki. Ya kamata mu ci gaba da amfani da darussan da muka ɗauko na taimakon juna da juriya da tausayi har bayan azumin na watan Ramadan,” in ji shi.
Tinubu ya kuma buƙaci Musulman ƙasar da su nuna ƙauna da son juna ta hanyar taimakon marasa ƙarfi ba tare da la’akari da bambancin addini ba, domin a cewarsa, hakan ne zai ƙara haɗa kan ƴan ƙasa.