Kwamishinan lafiya ta jihar kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya yi bayani akan manyan shirye-shirye da sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa don sauya fasalin tsarin kiwon lafiya a jihar Kano, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da manema labarai.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan kalubalen kiwon lafiyar da ake fuskanta a halin yanzu, matakan da gwamnati ke dauka, da kuma sabuwar kudurin cimma Universal Health Coverage (UHC) da inganta rayuwar al’umma baki daya.
A yayin shirin, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya jaddada kudurin Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na sanya lafiyar ‘yan Kano a sahun gaba cikin shirye-shiryen ci gaba na gwamnatinsa. Ya bayyana muhimman abubuwa 10 da gwamnati ke mayar da hankali a kai, wanda suka hada da:
- Kyakkyawan tsarin Samar da Magunguna Kyauta a asibitocin gwamnati, musamman a yankunan karkara, don saukakawa al’umma wajen kashe kudin jinya.
- Daukar Sabbin Ma’aikatan Lafiya da Yawa domin cike gibin ma’aikata a birane da yankunan karkara.
- Raba Uniform Kyauta ga Ma’aikatan Lafiya, don kara kwarewa, hadin kai da karsashi.
- Gyara da Gina Sabbin Cibiyoyin Lafiya a cikin birni da yankunan karkara.
- Bayar da Motocin Daukar marasa lafiya da na Aiki, don inganta agajin gaggawa.
- Horar da Ma’aikatan Lafiya, ta hanyar samar da damar karin ilimi a lokacin aiki.
- Samar da Na’urori na Zamani da Inganta Kayayyakin Asibitoci a matakin kiwon lafiya matakin farko da kuma mataki na gaba (Primary da Secondary Healthcare)
- Rage Kudaden Karatu a Fannonin Lafiya a makarantun gwamnati, don karfafa shigowar dalibai.
- Gyara Tsarin Gudanarwar Hukumar Kula da Asibitoci (HMB) don samun nagartaccen aiki da tsari.
- Karfafa Hadin Gwiwa da Kungiyoyin Cikin Gida da Na Kasa da Kasa, don dorewar sauye-sauyen.
Dr. Yusuf ya bayyana cewa wadannan matakai wani bangare ne na cikakken shiri da gwamnatin Kano ke aiwatarwa don samar da aminci cikin tsarin kiwon lafiya ga jama’a, tare da samar da kula da lafiyar da ta dace, mai rahusa da saukin samu ga kowa da kowa.
A nata bangaren, Dr. Rahila Aliyu Mukhtar ta bayyana nasarorin da Hukumar KSCHMA ta samu tun daga tsakiyar shekarar 2023 da yadda hakan ke kara bunkasa tsarin Taimakekeniyar lafiya.
Wasu daga cikin muhimman abubuwan da ta bayyana sun hada da:
Karin Masu Rijista da Fiye da Kashi 37%, wanda ya kara yawan masu amfana da Taimakekeniyar lafiya zuwa fiye da kashi 5.5% na al’ummar jihar.
Hadin Gwiwa da Shirin Sabatta Juyatta na Magunguna (DRF), wanda ke tabbatar da samuwar magunguna masu inganci a asibitocin da aka tantance.
Gabatar da Tsarin kula da bayanan marasa Lafiya ta Na’ura mai kwakwalwa (EMR) a wasu asibitocin gwaji, don inganta adana bayanai da aiki.
Shirin ABBA Care ga Marasa Lafiya musamman masu sikila, inda ake samar da magani kyauta da kulawa ga daruruwan marasa lafiya.
Wayar da Kai da Gwaje-Gwaje Kyauta ga Al’umma, tare da rijistar kan Taimakekeniyar Lafiya nan take a kananan hukumomi.
Dr. Rahila ta kara jaddada kudurin KSCHMA na kare hakkin lafiyar marasa galihu da tabbatar da cewa babu dan jihar da za a bari a baya sakamakon rashin kudi.