Jam`iyyar APC mai mulkin ƙasa, ta ce tana jin takaicin kayen da jam`iyyar NNPP ta yi mata a jihar Kano a zaben gwamnan da ya gabata.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shaida wa majiyarmu cewa, babban abin bakin ciki shi ne a ce sun rasa Kano.
Inda ya jingina rashin nasarar tasu a jihar Kanon da laifin wasu.
Shugaban na APC, ya ce Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba, wanda hakan ya sa ’yan jam’iyyar cikin wani hali saboda nasarar da jam’iyyar ba ta samu ba, duk da cewa su sun yi duk abin da ya kamata su yi.
Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Kano tana cikin jihohin da suke tunƙaho da ita, domin duk abin da za su yi Kano na kan gaba a lissafinsu.
Shugaban APCn, ya ce yanzu jira suke hayaniyar zabe ta lafa domin su dauki mataki a kan duk wanda ya yi wa jam’iyyar abin da bai dace ba.
Sanata Abdullahi Adamu, ya ce to amma duk da rashin nasara a Kano, suna gode wa Allah da Ya ba su nasara a zaben shugaban kasa da kuma wasu jihohin.
Ya ce, suna sa ran cinye Zaben ma da ake jira za a kammala a Adamawa da Kebbi