Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar rage yawan ciyo bashi yayin da take daɗa ƙoƙarin jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje zuwa Najeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da kafar yaɗa labarai ta Bloomberg TV a gefen taron Tattalin Arziki na Duniya (WEF) da aka gudanar a Davos, Switzerland, a ranar Talata.
Ya ce kodayake gibin kasafin kuɗin Najeriya ya ƙaru a rubuce bayan amincewar Majalisar Dokoki, yanzu gwamnati ta mayar da hankali kan daidaita harkokin kuɗi bayan aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa: “Amma kudurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan cire manyan matsaloli da daidaita tattalin arziki, shi ne a daidaita, a rage dogaro da bashi, sannan a ƙarfafa zuba jari daga ƙetare.”
A cewar ministan, halartar Najeriya a taron na Davos na nufin nuna sabuwar daidaituwar da tattalin arzikin ƙasar ya samu da kuma jan hankalin masu zuba jari.
Ana hasashen cewa biyan bashin na iya haura Naira tiriliyan 160 a ƙarshen shekarar 2025, yayin da gibin kasafin kuɗin 2026 ya kai sama da Naira tiriliyan 23.
Kwanan nan, Kwamitin Masana Tattalin Arziki na Daily Trust ya nuna damuwa kan yadda basussukan Najeriya ke ƙaruwa da sauri, inda ya kai Naira tiriliyan 152.39 (dala biliyan 99.66) a watan Yuni 2025, kuma na iya haura Naira tiriliyan 160 kafin ƙarshen shekarar.
Sun yi tambaya ko matakin basussun Najeriya zai iya dorewa, duk da cewa ƙarin bashin ya samo asali ne daga sabbin aro, tsadar riba a cikin gida, da kuma daidaita farashin musayar kuɗi.