Tinubu ya tura jakadu 4 daga cikin 68 da aka tantance

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura jakadu huɗu daga cikin jakadu 68 da Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da su a watan Disambar da ya gabata.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya amince da tura Ambasada Ayodele Oke a matsayin jakadan Najeriya zuwa Faransa, sai kuma Kanar Lateef Are a matsayin jakadan ƙasar zuwa Amurka.

Haka kuma, shugaban ya amince da tura Ambasada Amin Dalhatu, tsohon jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, a matsayin Babban Kwamishinan Najeriya zuwa Birtaniya.

Sai kuma Usman Isa Dakingari Suleiman, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, wanda aka tura a matsayin jakadan Najeriya zuwa Turkiyya, ƙasar da Shugaba Tinubu ke shirin kai ziyara ta musamman a mako mai zuwa.

Shugaban ya kuma umarci Ma’aikatar Harkokin Waje da ta sanar da gwamnatocin ƙasashen huɗu game da tura jakadun, kamar yadda dokokin hulɗar diflomasiyya suka tanada.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya