Mutane 16 Da Aka Kashe A Edo ’Yan Jihar Kano Ne — Amnesty

Ƙungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce mutane 16 aka kashe a mummunan kisan gillar jihar Edo ’yan asalin Kano ne, Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wani saƙo da Amnesty ta wallafa a shafukan sada zumunta ya bayyana cewa “’Yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fito da su daga motarsu, suka yi musu duka, sannan suka cinna musu wuta,”

Kungiyar ta ƙara da cewa matafiyan na kan hanyar komawa garinsu na asali ne “domin yin bukukuwan sallah tare da iyalansu.”

Amnesty ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar an hukunta masu hannu a kisan.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi