Mutane 764 Ke Kamuwa da Kansar Baki a Najeriya – Ministan Lafiya

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce cutar kansar baki da aka fi sani da kansar baka, na kashe mutane 764 a Najeriya duk shekara.

Ministan ya bayyana hakan ne jiya a Abuja yayin wani shirin horas da mutane yadda za su kare kansu daga cutar kansar baka wanda gidauniyar Cleft and Facial Deformity Foundation (CFDF) ta shirya.

Shugabar sashen kula da hakora na ma’aikatar lafiya, Dr Gloria Uzoigwe, ce ta wakilci ministan, inda ta ce ƙasar nan na samun sabbin masu kamuwa da cutar daji guda 1,146 a duk shekara.

Ta ce; ciwon daji na baka ya kasance daya daga cikin abubuwan da ke haifar da mace-mace mutane masu alaka da cutar daji a ƙasar nan saboda jinkirin rahoton da ake samu a asibitoci, da gazawar jami’an kiwon lafiya wajen gano cutar da wuri da kuma rashin isar da sako yadda ya kamata da dai sauransu.

Ministan ya ce gwamnati za ta kaddamar da wani sabon shirin kula da lafiyar baki a watan Nuwamba mai zuwa.

Post masu alaƙa

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.