Mutanen da suka mutu a haɗarin kwale-kwale a Sokoto sun kai 48

Kimanin mutum 48 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman yara 12 bayan haɗarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Goronya da ke jihar Sokoto.

Akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su yara ne waɗanda ke kan hanyar zuwa gona a safiyar jiya Alhamis.

A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gada da Goronyo a majalisar wakilan Najeriya Bashir Gorau ya ce a halin yanzu masu ninkaya na ci gaba da aikin ceto domin ganin ko za a samo sauran yaran da suka ɓace da ransu.

“Akasarin waɗanda abin ya rutsa da su yara ne da mata, yara ƴan ƙasa da shekara 10,” a cewar Gorau.

“Rafi ya raba mutanen ƙauyen da gonakinsu, shi ya sa a kodayaushe mutane ke amfani da kwale-kwalen katako domin zuwa gona,” kamar yadda ɗan majalisar ya yi ƙarin haske.

A Najeriya ana yawan fuskantar hatsarin kwale-kwale wanda ke laƙume rayuka musamman a yankunan karkara.

Lamarin ya fi ƙamari ne a lokacin damina, inda rafuka kan cika da ruwa, sannan kuma babu wasu matakan kariya da ake amfani da su wajen irin wannan sufuri, haɗi da rashin ingancin kwale-kwalen.

Post masu alaƙa

Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo

Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

Matasan Arewa sun bukaci gwamnonin arewa maso gabas su fi bai wa tsaro da samar da aikin yi muhimmanci