Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Dan’Azumi, ‘yar asalin Jihar Gombe murnar lashe gasar musabakar Alqur’ani bangaren mata ta duniya ta King Abdulaziz International Qur’anic Competition da aka gudanar a kasar Saudiyya.
Maryam ta zama ta farko a rukunin mata a gasar da aka gudanar a birnin Makkah, inda ta doke sauran mahalarta daga ƙasashe 132 na duniya.
Maryam ta samu riyalan Saudiyya 300,000, wanda ya yi daidai da kusan naira miliyan 120 a matsayin kyauta.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Maryam bisa ƙwarewa da bajintar da ta nuna wajen haddacewa, karatu da fahimtar Alƙur’ani mai girma. Ya ce nasarar ba ta Maryam kaɗai ba ce, inda ya ce ta zama abin alfahari ga Najeriya baki ɗaya, domin ta ɗaga darajar ƙasar a fagen duniya.
Tinubu ya kuma bayyana Maryam da ‘yar’uwarta, Hajara Ibrahim Dan’Azumi, a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya.
Hajara ita ma ta samu nasara a wata makamanciyar gasar Alƙur’ani da aka gudanar a Jordan a shekarar 2024, inda ta zo ta farko.
Shugaban Ƙasar ya yaba wa iyayensu, malamansu da masu kula da tarbiyyarsu, yana mai cewa irin wannan matsayi na ƙwarewa yana buƙatar sadaukarwa, jajircewa da kyakkyawar tarbiyya.
A ƙarshe, Tinubu ya yi wa Maryam addu’ar Allah Ya ƙara mata ilimi da hikima, Ya kuma ba ta damar ci gaba da samun nasara a karatun Alƙur’ani da sauran abubuwan da za ta gudanar a rayuwarta.