Mutum 29,314 ba su karɓi katunan zaɓensu ba a Taraba —INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce jimillar mutane 2,254,380 ne suka yi rajistar zaɓe a Jihar Taraba.

Kwamishinan INEC na jihar, Sa’ad Umar Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 da aka gudanar a Jalingo, babban birnin jihar.

Ya ce hukumar ta fara baje kolin sunayen masu rajistar zaɓe a dukkan mazabu da ƙananan hukumomi 16 na jihar, domin bai wa waɗanda suka yi rajista damar tantance bayanansu tare da tabbatar da sahihancinsu.

A cewarsa, har yanzu akwai katunan zaɓe guda 29,314 da masu su ba su karɓa ba, lamarin da ya bayyana a matsayin abin damuwa ga hukumar. Ya ce rashin karɓar katunan na nuna cewa wasu masu rajistar zaɓen ba za su iya kaɗa ƙuri’unsu ba a babban zaɓen shekarar 2027 idan ba su karɓi katunan ba.

Sa’ad Umar Idris ya ƙara da cewa daga cikin katunan zaɓen da ba a karɓa ba, akwai tsofaffin katuna guda 13,826 da aka yi wa masu su rajista tun shekarar 2011, amma har yanzu suna nan a ofisoshin hukumar ba tare da an zo an karɓe su ba.

Ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da raba katunan zaɓen a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi 16 na jihar daga ranar 19 ga watan nan zuwa ranar 30 ga wata mai zuwa, ban da ranakun hutu.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da sauran jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya dangane da harkokin zaɓe, saboda hakan na iya haifar da tashin hankali da barazana ga zaman lafiya.

Haka kuma, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula su bayar da gudunmawa wajen tabbatar da sahihin zaɓe a shekarar 2027.

Ya ce hukumar ta gudanar da gwajin na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS), kuma an samu nasarar gudanar da gwajin ba tare da wata tangarda ba.

A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Taraba, Edwin Ogbeghagha, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro za su samar da isasshen tsaro ga masu kaɗa ƙuri’a da sauran masu ruwa da tsaki a lokacin zaɓe.

Ya kuma gargadi ’yan siyasa da su ja kunnen magoya bayansu kan guje wa tayar da rikice-rikice a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma lokacin gudanar da zaɓe.

Ogbeghagha ya ce ya kamata ’yan siyasa su fahimci cewa siyasa ba ta kasance ta “a mutu ko a yi rai” ba, don haka ya buƙace su da su gudanar da harkokinsu cikin lumana domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zaɓe a faɗin jihar.

Post masu alaƙa

Ba na nadamar cire tallafin mai —Tinubu

Ambaliya ta kashe mutum 2, ta raba wasu 4,000 da gidajensu a Nasarawa

2027: Ba ma yi wa jam’iyyar APC aiki – Kwankwaso