N-Power: Gwamnatin tarayya za ta biya bashin hakkokin ma’aikata

Gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin cewa za ta biya waɗanda ke bin bashin haƙƙoƙinsu da ke cikin shirin nan da aka dakatar na N-Power, da kuma ba a kai ga biyansu ba.

Ministar hukumar Jinƙai da Yaƙi da Fattara, Betta Edu,  ce ta bayyana hakan a jiya ta hannun shugaban kula da shirin na N-power ta ƙasa, Akindele Egbuwalo.

A ranar Asabar ne, ministar ta sanar da dakatar da shirin saboda wasu dalilai da suka gano ake yi da ba su dace ba.

Inda ta ce akwai buƙatar a yi bincike game yawan waɗanda suke cikin tsarin da, da waɗanda suka kammala, da waɗanda ake suke bin albashi, da kuma ko su ma’aikatan na zuwa wuraren ayyukansu ka ba sa zuwa.

Sannan ta ce akwai buƙatar a gudanar da bincike game da yadda ake kashe kuɗaɗen da ake warewa shirin na N-Power.

Inda ta buƙaci ‘yan Najeriya da su kalli wannan dakatarwar da idon basira tare da fahimtar dalilai da suka tilasta dakatar da shirin.

A ƙarshe, ta ba da tabbacin cewa da zarar an kammala tantance waɗanda ke bin bashin haƙƙoƙinsu.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr