Ɓarayi sun sace sarƙa mai shekaru 2,500 daga gidan kayan tarihi a Faransa

Ɓarayi sun sace wani tsohon abin wuya na zinariya mai kimanin shekaru 2,500 daga wani gidan kayan tarihi da ke garin Chatillon-sur-Seine a yankin Burgundy na ƙasar Faransa.

Masu gabatar da ƙara sun ce lamarin ya faru ne da rana tsaka, inda ’yan fashin suka fasa gilashin da aka ajiye kayan tarihin a ciki, sannan suka tsere da abin wuya.

Magajin garin, Jeremie Brigand, ya ce an taɓa yunƙurin satar kayan tarihin sau biyu a baya-bayan nan, lamarin da ya sa aka ƙara tsaurara matakan tsaro.

Sai dai ya ce a wannan karon ɓarayin sun zo da shiri wanda suka aiwatar cikin gaggawa duk da kasancewar ma’aikata, baƙi da jami’an tsaro a wurin.

Abin wuyan da aka sace yana da nauyin kusan rabin kilogram, kuma a zamanin Keltawa da Goliya ana amfani da shi a matsayin abin ado da ke nuna alamar iko.

Sarƙar wuyan na daga cikin tarin kayan tarihi na Vix Treasure, waɗanda aka gano a kabarin wata gimbiya a ƙauyen Vix a shekarar 1953.

Post masu alaƙa

Amurka za ta sayar wa Saudiyya makamai na dala biliyan 5

Nijar ta zargi Faransa ta kitsa juyin mulki a ƙasar

Duk wanda ke da hannu a harin Amurka kan tsibirin Larak zai ɗanɗana kuɗarsa – Iran