Rahotanni daga yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da ke Jihar Katsina sun ce jami’an tsaro sun kashe wasu manyan kwamandojin ’yan bindiga biyu a wani artabu da suka yi da ’yan ta’addan da ke ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira Kachalla Fulani.
Majiyoyi sun ce artabun ya biyo bayan wani harin kwanton ɓauna da ’yan bindigar suka kai garin Matazu a lokacin Sallar Magariba ta shekaranjiya Asabar.
Rahotannin sun ce farmakin da jami’an tsaron suka kai wa maharan ya yi sanadin mutuwar Mamiyo, mai kimanin shekaru 25, da Naziru, mai kimanin shekaru 19, waɗanda ake zargin suna daga cikin manyan na hannun daman Kachalla Fulani.
Mamiyo dai ana zargin shi ne babban mataimakin Kachalla Fulani kuma na hannun damansa, wanda ke jagorantar wasu hare-hare a yankin.
Shi kuwa Naziru, wanda aka ce yana da kimanin shekaru 19, na daga cikin mutanen da Kachalla Fulani ya dogara da su wajen kai hare-hare.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wani bayani da hukumomin tsaro suka fitar a hukumance kan kisan mutanen biyu ko kuma ƙarin bayani kan artabun.
Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa yankin Matazu na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka ƙara gudanar da samame a yankin.