Netumbo Nandi Ta Zama Mace Ta Farko Da Zata Jagoranci Shugancin Kasar Namibia

An rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin shugabar ƙasar Namibia, wadda ta kafa tarihin zama mace ta farko da za ta jagoranci ƙasar.

Tshohuwar ministar harkokin wajen ƙasar ta kasance jajirtaciyyar ƴar jam’iyyar SWAPO wadda ke mulkin Namibia tun bayan samun ƴancin kai daga Afirka ta Kudu a 1990.

Da take magana da BBC, Nandi-Ndaitwah ta yarda da cewa wasu za su iya sukarta saboda jinsinta maimakon ayyukan da take yi – sai dai ta ce za ta ci gaba da yaƙi da cin zarafin jinsi.

Netumbo ta shiga cikin jerin matan Afirka ƙalilan da suka jagoranci ƙasarsu tun lokacin da Liberia ta zaɓi shugabar ƙasa ta mace ta farko shekaru 20 da suka wuce.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.