Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen samun mabambantan yanayi a wasu sassan ƙasar, da suka haɗa da hazo da ruwan sama daga Litinin zuwa Laraba.
Cikin wani rahoto da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta buƙaci ƴanƙasar su zama cikin shiri domin tunkarar waɗannan yanayi.
NiMet ta yi hasashen samun hazo har na tsawon kwana uku a jihohin Borno da Zamfara da Yobe da Jigawa da Kano da Katsina da kuma wasu yankunan arewacin Kaduna.
Haka ma hukumar ta ce akwai hasashen samun ruwan sama haɗe da tsawa a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa.
Hukumar ta kuma yi hasashen samun rana a wasu jihohin arewa ta tsakiyar ƙasar, da kuma yiwuwar samun ruwan sama a jihohin Nasarawa da Kogi da Birnin Tarayya Abuja.