• Home  
  • Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa, ya ce zai kare kansa a kotu
- Babban Labari - Labarai

Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa, ya ce zai kare kansa a kotu

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa. A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba. Lauyoyin da ke kare shi ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun yanke hukuncin cire hannunsu daga […]

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa.

A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba.

Lauyoyin da ke kare shi ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun yanke hukuncin cire hannunsu daga kare shi kan shari’ar da yake fuskanta.

Daga nan sai Kanu ya fara magana kai-tsaye, inda ya ƙalubalanci ikon kotu na ci gaba da yin shari’arsa.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000