Kamfanin mai na NNPC, ya ce jama’a su daina fargaba domin akwai wadataccen mai a kasa
Wannan na zuwa ne bayan da aka fara samun layin mai da aka fara dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassa na Najeriya bayan sanarwar cire tallafin mai da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi.
Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari, ya ce, akwai mai don haka babu wata matsala da ya ke gani za a iya fuskanta da ta shafi karancin man.
Ya ƙara da cewa dama duk lokacin da aka samu irin wannan jawabi daga shugabanni, sai mutane su yi ta tururuwa suna zuwa gidajen mai suna siyan mai fiye da wanda suke bukata
saboda suna tsoron kada a kara kudin man a cewar.
Ya kara da cewa bai ga abin tsoro ba domin akwai mai sosai a kasa.