Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyar Al-Muhajirun Humanitarian Development Association domin kare hakkin yara da tallafawa bangarorin al’umma masu rauni.
Wannan na zuwa ne daidai lokain da wakilan kungiyar Al-Muhajirun sun kai ziyarar ban girma heldikwatar NOA da ke Abuja, inda babban Daraktan hukumar, Malam Lanre Issa-Onilu, ya sanar da cewa hukumar ba kawai tana isar da manufofin gwamnati ba ne, wata hanya ce ta dawo da sakonni daga jama’a zuwa ga gwamnati.
Issa-Onilu ya ce NOA na da niyyar kara karfafa muradun marasa galihu ta hanyar isar da korafe-korafen halin da suke ciki ga gwamnati, domin samar da hanyoyin magance matsalolin su tare da irin dokoki ko manufofin da suka dace.
- Yan Ta’adda Na Kafa Doka Da Karɓar Haraji A Arewa — Dambazau
- An Kammala Kilomita 39 A Titin Abuja-Kaduna-Kano – Gwamnati
A nasa bangaren, Shugaban Hulda da kungiyar Al-Muhajirun, Jakada Anas Maitamanin, ya yaba wa Babban Daraktan NOA bisa jajircewarsa wajen tallafa wa ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ayyukan NOA sun yi daidai da muradun kungiyar wajen kare hakkin yara, samar da zaman lafiya da kuma wayar da kan jama’a a kan muhimman batutuwan zamantakewa.
