Hukumar wayar da kan Jama’a ta kasa (NOA) ta lashe kyautar kamfen ɗin wayar da kan jama’a ta shekarar 2026, a bikin bayar da kyaututtuka na musamman na hukumar kula da harkokin tallace-tallace ta Najeriya (ARCON).
An gudanar da bikin ne ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, a cibiyar taro ta Balmoral da ke Ikeja, a jihar Legas.
Babban Daraktan NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, wanda Daraktan Sadarwa da yaɗa labarai na hukumar, Bala Musa, ya wakilta, shi ne ya karɓi lambar yabon a madadin shugaban hukumar.
Kyautar ta nuna irin gudummawar da hukumar ke bayarwa wajen wayar da kan jama’a, ilimantar da su kan harkokin mulki da kuma yaɗa manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Da yake tsokaci kan kyautar, Issa-Onilu ya ce wannan karramawa ta ƙara ƙarfafa aniyar hukumar na inganta hanyoyin sadarwa da jama’a, bunƙasa kishin ƙasa da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da amfani da gidajen rediyo da talabijin, kafafen sadarwar zamani da sauran hanyoyin sadarwa wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa kyawawan ɗabi’u.
Babban daraktan ya miƙa godiyarsa ga ARCON bisa wannan karramawa, tare da yaba wa ma’aikatan hukumar a faɗin ƙasar, musamman waɗanda ke aiki a matakin ƙananan hukumomi, bisa gudummawar da suke bayarwa.