• Home  
  • NOA ta yi martani kan rahoton Nairamatrics game da shigowar jari Najeria
- Babban Labari

NOA ta yi martani kan rahoton Nairamatrics game da shigowar jari Najeria

  Hukumar Wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) ta bayyana cewa nazarin da Nairametrics ta yi kan rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) game da shigowar jarin waje a zangon farko na shekarar 2026 bai bayyana cikakken rahoton ba. NOA ta ce rahoton NBS yana ƙirga ne kawai jarin da ya shigo ta bankunan […]

 

Hukumar Wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) ta bayyana cewa nazarin da Nairametrics ta yi kan rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) game da shigowar jarin waje a zangon farko na shekarar 2026 bai bayyana cikakken rahoton ba.

NOA ta ce rahoton NBS yana ƙirga ne kawai jarin da ya shigo ta bankunan Najeriya, ba ya haɗa da jarin da kamfanoni ke kawowa kai tsaye daga ƙasashen waje, kuɗaɗen da ake sake zuba wa a kamfanoni, ko kuma kuɗaɗen manyan ayyukan man fetur da ake ɗaukar nauyinsu daga ƙasashen waje.

Hukumar ta amince cewa mafi yawan dala biliyan 10 da suka shigo Najeriya a zangon farko na 2026 sun tafi ne kan harkokin kasuwar kuɗi, ba kai tsaye wajen gina masana’antu ko samar da ayyukan yi ba.

Sai dai ta ce wannan ba yana nufin babu manyan jarin ci gaba a ƙasar ba.

NOA ta ƙara da cewa rahoton Nairametrics ya yi daidai wajen lissafi, amma bai yi cikakken bayani kan sauran manyan jarin cikin gida da na waje da ke tallafa wa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

A cewar NOA, domin a fahimci ci gaban tattalin arzikin Najeriya yadda ya kamata, ya zama dole a duba ba kawai adadin jarin da ya shigo ba, har ma da hanyoyin da yake bi da kuma yadda ake amfani da shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai