A ranar Juma’a 21 ga Maris ne ake bikin Ranar Masu Larurar Galahanga ta Duniya, wato Down Syndrome a Turance.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta amince da kowacce ranar 21 ga watan Maris domin wayar da kan jama’a game da lalurar, tare da ƙoƙarin gano matsaloli da masu galahanga ke fuskanta, da kuma me za su iya yi, ranar ta samo asali ne tun a shekarar 2012.
Galahanga dai ana haifar yaro ne da wasu ƙarin kwayoyin halitta. Yanayin kwayoyin halittar yawanci na shafar koyon wani abu da zai yi da kuma yanayin jikinsa.
Lalurar ba cuta ba ce, illa rashin lafiya ko yanayin da wani zai iya kamuwa da shi.
Ba a dai san me yake haddasa lalurar ba – saboda kawai haifar mutum ake yi da ita.
Yawanci mutanen da aka haifa da lalurar suna samun ƙarin kwayoyin halitta, saboda canjin maniyyi ko kwai kafin a haife su.
Ana samun waɗanda ake haifa da lalurar ko’ina a yankuna da ke faɗin duniya. kuma galibi tana yin tasiri a kan salon koyo, halayen jiki da kuma lafiya, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ana haifar jariri ɗaya cikin 800 da galahanga, a cewar masu shirya bikin Ranar Galahanga ta Duniya .
A halin yanzu dai babu maganin lalurar.
Ana iya ba da taimako bisa la’akari da buƙatun kowane mutum kama daga tunani, ƙarfi, da kuma gazawa.
Samun isassun hanyoyin kula da lafiya, shirye-shiryen bayar da taimako da kuma ilimi, da kuma binciken da ya dace, na da muhimmanci ga ci gaban masu wannan ciwo na galahanga, in ji MDD.
Taken bikin na wannan shekara shi ne Inganta Tsarin Tallafin masu galahanga.ƙarfafa haɗa kai don tabbatar da cewa masu fama da wannan ciwo na galahanga sun sami kulawa, ilimi, da damar da suka cancanta.