Real Madrid Ta Sanar Da Daukar Alonso A Matsayin Sabon Kocinta

Real Madrid ta sanar da ɗaukar Xabi Alonso a matsayin sabon kocinta.

Alonso wanda ya buga wa Real ɗin wasa 236 a matsayin ɗan wasanta a baya, ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku.

A farkon watan nan ne ya sanar da cewa zai bar Bayer Leverkusen da yake jagoranta.

Tsohon ɗan wasan na Liverpool da kuma Sifaniya, ya jagoranci ƙungiyar lashe kofin Bundesliga a bara ba tare da an doke shi ko da wasa ɗaya ba – da kuma German Cup.

Alonso wanda yarjejeniyarsa za ta kai har 30 ga watan Yunin 2028, zai maye gurbin Carlo Ancelotti.

Ancelotti ya jagoranci wasansa na karshe a Madrid a ranar Asabar, inda a yanzu zai zama sabon kocin ƙasar Brazil.

Za a gabatar da Alonso wanda ya lashe Champions League a 2014 lokacin da yake buga wa Madrid kwallo – a gobe Litinin a filin atisayen ƙungiyar.

Post masu alaƙa

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC