Daga Muazu Hardawa, Bauchi.
Hukumar zabe Mai zaman kanta a jihar Bauchi BASIEC ta gudanar da zaben cike gurbi a karamar hukumar Shira a ranar asabat 24 ga watan Mayu 2025.
Tun a ranar jumaah 23 ga watan Mayu hukumar ta BASIEC ta raba muhimman kayayyakin gudanar da zaben a karamar hukumar Shira don cike gurbin shugaban karamar hukumar wanda Kansiloli suka tsige shi tare da mataimakin sa a kwanakin baya.
Shugaban hukumar zabe Mai zaman kanta a jihar Bauchi BASIEC, Alhaji Ahmed Makama shine ya jagoranci raba kayan zaben ranar jumaah a harabar ofishin hukumar a Bauchi, kuma ba tare da bata lokaci ba aka kwashi kayan da suka hada da akwatunan jefa guri’a da takardun zabe da sauran muhimman kayan aikin zaben zuwa karamar hukumar ta Shira.
A ranar asabat da safe mutane suka fita rumfunan zabe guda 249 yadda jami’an zaben suka gudanar da aikin zuwa yammaci bayan an kammala, jagora mai tattara zaben Malam Kabiru Abba ya kawo sakamakon zuwa ofishin hukumar da ke Bauchi.
Shugaban hukumar zaben Alhaji Ahmed Makama ya bayyana jam’iyyun siyasa uku ne suka shiga zaben.
Cikin su akwai jam’iyyar ADC wacce Yakubu Ayuba ya tsaya takara tare da mataimakin sa Sulaiman Ibrahim Datti, yadda suka samu guri’u 241.
Sai Kuma jam’iyyar YPP wacce Shafi’u Haladu ya tsaya takara da mataimakin sa Bello Garba Kuma sun samu guri’u 293.
Sai Jam’iyyar PDP mai Mulki a jihar Bauchi wacce Babangida Ishak Abdullahi Maliya, ya tsaya takara tare da mataimakin sa Ali A. Adamu Kuma sun samu nasara da guri’u dubu 47,361 yadda suka lashe zaben da gagarumin rinjaye.
Jam’iyyar APC babbar Mai adawa a jihar Bauchi bata samu shiga zaben ba. Kuma tun farko ta bayyana rashin gamsuwa da yadda aka shirya gudanar da zaben, don haka ta rubuta takardar janyewa daga shiga zaben zuwa ga hukumar ta BASIEC.
Wata majiya Mai tushe ta bayyana mana cewa bayan haka Kuma sun garzaya kotu yadda suka bukaci a dakatar da gudanar da zaben har sai an yi gyare gyaren da za su gamsu. Majiyar ta bayyana mana tuni kotun ta sa watan Yuni wato June don fara sauraron karar.
- Real Madrid Ta Sanar Da Daukar Alonso A Matsayin Sabon Kocinta
- Yan Sanda Sun Gaiyaci Harrison Gwamnishu Kan Wallafa Batan Mutane A Anambra.
Dukkan kokarin da muka Yi don jin ta bakin shugabannin jam’iyyar ta APC ya ci tura. Amma a duk lokacin da muka ji daga gare su za mu sanar da jama’a.
Bayan kammala sanar da sakamakon zaben a harabar hukumar ta BASIEC a Bauchi a yammacin asabat a gaban kwamishinonin hukumar da sauran ‘yan siyasa da ‘yan gudu, shugaban hukumar ta BASIEC Alhaji Ahmed Makama ya bayar da takardun shaidar cin zaben wa Alhaji Babangida Ishak Maliya da mataimakin sa Ali A. Adamu.
Kuma ya bayyana cewa an Yi zaben lafiya an gama lafiya, Kuma mutane sun fito sosai fiye da sauran zabukan gama gari da suka gudana kwanakin baya a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi.
Don haka Ahmed Makama ya yi fatar Alheri da Neman Allah ya ba sabbin shugabannin karamar hukumar ta Shira iko da damar gudanar da jagoranci bisa bin doka da adalci da nuna gaskiya ga mutanen da suka zabe su cikin nasara.