Wata sabuwar dambarwa ta sake tasowa a cikin gidan jam’iyyar APC a jihar Kano, kwanaki kaɗan bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa.
Wasu ƴaƴan jam’iyyar sun fito suna neman shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas wanda na hannun daman Ganduje ne, ya sauka daga muƙaminsa, lamarin da ɓangaren Abdullahi Abbas ke zargin jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano da ingiza wa domin cimma wani buri nata.
Ko da yake ba ba wannan ne karon farko da APCn ke fama da rikicin cikin gida a Kano ba, wannan karon rikicin ya ɗauki sabon salo kuma ana alaƙanta shi da saukar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar a matakin tarayya.

