Rundunar kishin Kano RKK ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Ibrahim Sani mai ritaya ta ƙulla alaƙar aiki da gidan Talabijin da Rediyo na MUHASA domin yaƙi da Shaye-shaye da sauran miyagun laifuka ta hanyar gabatar shirye-shiryen wayar da kai a jihar.
Shugaban ƙungiyar, Manjo Janar Ibrahim ya bayyana cewa tashar tashoshin MUHASA na da inganci da kayan aikin iya sauya tunanin mutane cikin sauƙi, lura da tarin masu kallo da masu sauraron tashar.
Manjo Janar Ibrahim Sani ya ce” Ina ganin ayyukan tashar, ashe ma tamu ce, Muhammad Babandede ɗan uwana ne, abokin gwagwarmaya.
“Rundunar kishin jihar Kano tana gudanar da ayyukan wayar da kan matasan mu kan illolin Shaye-shaye, da daba, da zaman kawai.
“Mun shirya wasan kwaikwayo mai suna “Babbar Mafita” wanda ke yaƙi da Shaye-shaye da bautar da ɗan Adam, muna so tashar talabijin da rediyo na MUHASA su dubi yadda za su shigo lamarin domin”.
- An Yanke Wa Barawon Keke Zaman Gidan Yarin Shekara 1 A Filato
- Kotun Kolin Nijeriya Ta Yanke Hukunci Kan Dokar Yancin Samun Bayanai FOIA 2011.
Da yake tsokaci kan buƙatar ta RKK Muhammad Babandede OFR, OCM ya bayyana manufar ƙungiyar a matsayin irin ta MUHASA, ya kuma godewa Manjo Janar Ibrahim Sani kan yadda yake hidima da dukiyarsa, da ƙwarewasa wurin lalubo hanyoyin inganta rayuwar al’ummar Kano.
“Hakika manufar RKK ta yi kama da manufar MUHASA, in sha Allah za mu yi aiki tare domin inganta rayuwar al’ummar Kano da ma Arewacin Najeriya.
“Ina godiya da ga Manjo Janar Ibrahim Sani, hakika kana abin da ya dace, zaka samu lada duniya da lahira”.
Manjo janar Ibrahim ya ce, wasu daga cikin ‘yan daban da suka yarda da shawarwarin RKK sun samu abin yi, har sun fara taimakawa iyayensu.