Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ƙara tsaurara tsaro a bikin Easter.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamishinanta, CP Ibrahim Adamu Bakori, ta taya Kiristoci murnar bikin Easter tare da tabbatar da cewa an tanadi isasshen tsaro a duk faɗin jihar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce, an tura jami’an ƴan sandan  zuwa wuraren ibada da sauran muhimman wurare domin tabbatar da tsaro da  zaman lafiya yayin gudanar da bikin.

Haka zalika, an umurci shugabannin sassan rundunar da suka hada da kwamandodjin ƴan sanda da baturan ƴan sanda su ƙara tsaurara matakan tsaro da sanya ido.

A ƙarshe rundunar ta buƙaci jama’a a duk lokacin da suka ga wani abu da amince dashi ba, su gaggauta sanarwa a ofishin ƴan sanda mafi.

 

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.