Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama mutane 345 da ake zargi da aikata laifukan Daba da dillalan ƙwaya da kuma waɗanda aka samu da mallakar muggwan makamai.
Kwamishinan ƴan sandan jihar kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yiwa manema labarai ƙarin haske a shelkwatar rundunar dake Bompai.
CP Bakori ya ce sun gudanar da aikin daga ranar juma’a zuwa ranar Lahadi , inda suka mayar da hankali kan wuraren da ake aikata laifuka da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Haka zalika ya ƙara da cewa an samu nasarorin ne sakamakon kyakkyawan shirin da suka yi don tabbatar da zaman da tsaro zaman lafiya, domin jihar Kano cibiyar Kasuwanci ce da kuma al’adun hausa, wajibi ne a samar da kyakkyawan tsari na tsaro wanda zai dogara kan samun bayanan sirri da kuma aiki tare da al’umma, bisa umarnin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, rundunar ƴan sandan Kano ta ƙara ƙaimi wajen magance laifuka.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa makamai masu haɗari guda 270 ciki harda Wuƙaƙe da Adduna, Gatari da sauran kayan da ake amfani da su wajen tashin hankali.
Kazali an ƙwato haratattun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar Wiwi, ƙwayoyin Exol da Pregabalin da madarar Sukudayin da sauran kayan maye.
Kwamishina ya ce nasarorin da aka samu sun taimaka wajen hana faɗan daba da aikata manyan laifuka kamar fashi da makami da ƙwacen waya da sauransu.
Rundunar ta ce manyan shirye-shiryen ta na Operation Kukan Kura yaƙara yawan sintirin ƴan sandakan tituna da kuma sabon sashen magance manyan laifuka VCRU, da aka ƙaddamar a kwanakin baya ya ƙara ƙarfin dakarun da kuma tattara bayanan sirri.
A ƙarshe ya godewa gwamnatin jihar Kano, bisa goyon baya da haɗin kai da ya taimaka wajen gudanar da aiyukan , tare da godewa al’ummar jihar bisa addu’o’insu koda yaushe.