Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta raba ₦13,353,589.45 ga iyalan jami’anta da suka rasu.

Rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ta raba Naira miliyan goma sha uku da dubu ɗari 353 da 589 da kobo 45 (₦13,353,589.45) ga iyalan jami’an da suka rasu, a bakin aiki a matsayin wani ɓangare na bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina,DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya raba wa manema labarai.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ali Umar Fage, ya ce rundunar na ci gaba da kula da jin daɗin jami’anta da iyalansu, tare da roƙon waɗanda suka amfana su yi amfani da kuɗin yadda ya dace.

Iyalan jami’an ƴan sanda 15 ne suka amfana da tallafin, inda bayyana godiyarsu, bisa kulawar rundunar ƴan sandan ke yi mu su.

 

Post masu alaƙa

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .