• Home  
  • Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana damuwa kan mutuwar Janar Rabe a hannun ƴan bindiga
- Babban Labari

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana damuwa kan mutuwar Janar Rabe a hannun ƴan bindiga

A saƙon jaje da rundunar tsaron Najeriya ta fitar, ta bayyaa rashin a matsayin babba, inda ta ce za ta ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar baki ɗaya. “Muna miƙ saƙon ta’aziyya da jaje kan rasuwar abokin aikinmu Manjo Janar Abubakar ga iyalansa da sauran ƴan Najeriya baki ɗaya. A lokacin da yake […]

A saƙon jaje da rundunar tsaron Najeriya ta fitar, ta bayyaa rashin a matsayin babba, inda ta ce za ta ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar baki ɗaya.

“Muna miƙ saƙon ta’aziyya da jaje kan rasuwar abokin aikinmu Manjo Janar Abubakar ga iyalansa da sauran ƴan Najeriya baki ɗaya. A lokacin da yake aiki a matsayin mai magana da yawun rundunar tsaro, ya taimaka matuƙa wajen yaƙi da matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta.”

Rundunar ta ƙara da cewa jajircewarsa da ƙoƙarinsa wajen tabbatar a zaman lafiya da haɗin kan Najeriya abin koyi ne babba.

Sai dai rundunar ta ce sun yi shiru ne game da sacen shi da aka yi saboda yunƙurin da ake yi ne ceto shi, inda jami’an tsaron Najeriya sun kasance suna ta ƙoƙarin tabbatar da ceto shi cikin ƙoshin lafiya.

“Mutuwarsa za ta sa jami’anmu su ƙara ƙaimi wajen cigaba da aiki ba dare ba rana domin kare martabar ƙasarmu Najeriya da kuma tabbatar da kariyar al’ummar ƙasar baki ɗaya,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “muna tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da tsaro a ƙasar, tara da cimma duk waɗanda suke da hannu a matsalolin tsaro.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai