Rahotanni daga Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano na cewa mamakon ruwan sama mai karfin gaske da iska sun janyo rushewar gidaje a garin Dogon Jeji.
An bayyana cewa ruwan ya yaye rufin dakuna da yawa in da ya bar masu su cikin halin rashin tabbas.
Malam Isah Muhammad, ya shaida wa Arewa Updates cewa lamarin ya faru ne da yammacin Laraba, inda cikin kankanin lokaci iska da ruwan sama suka yi barna mai tarin yawa.
Malam Isa ya ce, “Gidaje da dama sun rushe, kuma rufin dakuna da yawa sun yaye. Gaskiya jama’a sun shiga cikin wani hali,” .
- Za A Samu Fari A Jihohi 9 Na Arewacin Najeriya A Tsakiya Daminar 2025
- Za A Yi Zanga-zanga A Jihohi 20 Na Najeriya Gobe Alhamis
Abdul Goma wani dan jarida da ke zaune a garin ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an tafka asara mai yawa.
Wannan dai ba shine karo na farko da ruwa ke yin gyara a yankunan jihar Kano ba a bana.