Najeriya da Amurka sun ce sun sake kai jerin hare-hare kan sansanonin mayaƙan ISIS da ke arewa maso gabashin Najeriyar a wani ɓangare na ayyukan fatattakar masu iƙirarin Jihadi a yankin.
Amurka ta ce an kai hare-haren ne ranar Lahadi bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun ce samamen na baya-bayan nan an ƙaddamar da su ba tare da wata matsala ba a yankin Metele da ke jihar Borno.
A cewar sojojin, an kai samamen ne bayan da aka gano taruwar ƴan ta’adda a wajen inda suka ce hare-haren sun halaka fiye da mayaƙan Iswap da Isis 20.
Hare-haren na baya-bayan nan na zuwa ne kwana ɗaya bayan wani hari na haɗin gwiwa na Najeriya da Amurka wanda ya yi sanadin mutuwar Abu Bilal al-Minuki, da ƙasashen biyu suka bayyana shi a matsayin ƙusa a ƙungiyar Isis.
Hukumomi sun ce samamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin murƙushe mayaƙan.
Cikin wata sanarwa da aka fitar yau Litinin, rundunar Amurka da Afirka, Africom ta ce bayanan sirri da aka tattara sun tabbatar cewa mayaƙan Isis ne a wajen sannan kuma babu wani sojin Najeriya ko Amurka da lamarin ya shafa.
Rundunar ta ce kashe mayaƙan na ƙara raunana ƙarfin ƙungiyar na shirya share-hare da ke barazana ga tsaron Amurka da ƙawayenta.

