Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.

Ministan jarkokin yan danda na Najeriya, Sanata Ibrahim Gaidam, ya ce sabuwar majalisar Gudanarwar makarantar horas da yan sanda ta Najeriya, POLAC da ke Wudil, za ta mayar da hankali wajen inganta ilimi da horo da kuma amfani da fasahar zamani.

Gaidam, wanda shi ne shugaban majalisar, ya bayyana hakan ne yayin taron farko na sabuwar majalisar da aka gudanar a makarantar.

Ya ce POLAC na da muhimmiyar rawa wajen samar da jami’an ‘yan sanda masu ƙwarewa, ɗa’a da sanin aikinsu.

Ya ce za a ƙarfafa horo kan yaƙi da laifukan yanar gizo, binciken laifuka, kare haƙƙin ɗan Adam da hulɗa da jama’a, tare da inganta bincike da kirkire-kirkire.

Ministan ya ce burinsu shi ne ganin POLAC ta zama mai inganci wajen samar da ƙwararrun jami’an ‘yan sanda da za su iya kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da bin doka.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.